in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shawo kan cutar makanta a gabashin Sudan
2018-11-19 10:34:20 cri
Ma'aikatar lafiya a kasar Sudan, ta ce yankin Gallabat na jihar Qadarif dake gabashin kasar, ya kubuta daga cutar makanta da wani nau'in kuda ke yadawa.

Ma'aikatar lafiyar ta ce an cimma nasarar kawar da cutar daga yankin Gallabat ne, bayan cin galabar ta a yankin Abu Hamad dake arewacin kasar.

Da yake tabbatar da hakan yayin wani taron 'yan jarida a birnin Khartoum, fadar mulkin kasar, ministan lafiyar kasar Mohamed Abu Zaid Mustafa, ya ce tun a shekarar 2007 aka fara gangamin yaki da wannan cuta ta makanta, a yankin Gallabat mai nisan kilomita 566 daga gabashin birnin Khartoum. Mr. Mustafa ya ce binciken masana da aka gudanar tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015 ya nuna cewa, cutar makantar ta daina yaduwa a yankin

Cutar makanta ta "River blindness" wani nau'in kuda ne ke yada ta, ta hanyar yada wasu kwayoyin cuta da ake cewa "Onchocerca volvulus" a turance, kuma alamomin ta sun hada da kaikayi mai tsanani, da kunburin fatar jiki, kafin wadanda ya kamu da ita ya kai ga makancewa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China