Tut Gatluak, mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan harkokin tsaro, ya fadawa 'yan jaridu a jiya Litinin cewa, gwamnatin Sudan da kungiyoyin 'yan tawayen kasar sun amince da tayin da Juba ta yi musu na shiga tsakani don tattaunawar sulhun, wanda ake sa ran gudanarwa a makon gobe.
Kasar ta Sudan ta jima tana fuskantar rikici da kungiyoyin 'yan tawaye masu fafutukar ceto al'ummar Sudan wato (SPLM-N) a kudancin Kordofan da jahar Blue Nile tun a shekarar 2011.
An sha yunkurin shirya tattaunawar sulhu a lokuta da dama da nufin kawo karshen tashin hankalin dake cigaba da ta'azzara a yankunan biyu na kan iyakokar Sudan da Sudan ta kudun amma al'amarin ya ci tura. (Ahmad)