in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai dace a zargi Sin bisa taimakon da take ba kasashen Afirka ba, in ji shugaban Zimbabwe
2018-12-01 16:53:59 cri
An kaddamar da bikin fara ginin babban zauren majalisar dokokin kasar Zimbabwe, wanda kasar Sin ta dauki nauyin ginawa a Harare, babban birnin kasar.

Da yake jawabi yayin bikin da ya gudana a jiya, shugaban kasar Emmerson Mnangagwa, ya godewa kasar Sin da al'ummarta dangane da taimakonta ga kasar Zimbabwe a fannin ginin ababen more rayuwa.

Sannan, ya yabawa shawarar ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta fidda, wadda ta taimaka matuka ga kasashen Afirka, wajen samar da ababen more rayuwa, kamar yadda ake gina zauren majalisar dokokin kasarsa.

Ya kara da cewa, bai kamata a zargi kasar Sin saboda taimakon da ta ke ba kasashen Afirka ba. yana mai cewa, akwai wasu kasashen duniya da ba su amince da taimakon da kasar Sin ke ba kasashen Afirka ba, sai dai zargin da suke yi wa kasar Sin ba shi da tushe. Ya kara da cewa, yayin ziyararsa a kasar Sin a bana, ya hadu da wasu mutane masu neman jari a birnin Beijng, wadanda suka taba fada masa cewa, ba za su zo Beijing ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China