Mukaddashin jakadan Sin dake kasar Zimbabwe Zhao Baogang ya halarci bikin tare da yin jawabi, inda ya bayyana cewa, kasar Sin aminiya ce ta kasar Zimbabwe, wadda ta samar da taimako da dama wajen raya kasar Zimbabwe. Yanzu kasar Zimbabwe tana kokarin kawar da yanayin raguwar bunkasuwar tattalin arziknta, gina kamfanin zai taimakawa kasar Zimbabwe wajen raya tattalin arziki da amfanawa jama'a tare da sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Zimbabwe.
An ce, kamfanin zai samar da ayyuka fiye da dubu daya ga kasar Zimbabwe. Yanzu ana gina kamfanin, ana sa ran za a gama gina shi da fara kera fadi-ka-mutu a tsakiyar shekarar badi. (Zainab)