in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe za ta karbi bakuncin taron fasahar sadarwa na Afirka
2018-11-27 19:10:03 cri

A gobe Laraba ne ake sa ran shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, zai jagoranci kaddamar da taron yini biyu, na karawa juna sani game da fasahar sadarwa a nahiyar Afirka.

Kimanin baki sama da 500 ne ake sa ran za su halarci taron daga kasashen Afirka 17, da sauran kamfanoni na kasa da kasa 45 da batun ya shafa, ciki hadda Microsoft, da Intel, da JP Canon, da dai sauran su.

Da yake tabbatar da hakan a Talatar nan, minista a ma'aikatar ilimin firamare da sakandare na kasar Paul Mavima, ya ce ma'aikatar sa da hadin gwiwar wasu kamfanoni masu zaman kan su biyu ne za su dauki nauyin gudanar da taron.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China