in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya bukaci a dauki tsauraran matakai yayin da hatsarin mota ya sake yin sanadin rayuka 42
2018-11-17 16:07:42 cri
Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya aike da sakon jaje a jiya Juma'a, bayan wasu mutane 42 sun mutu a daren ranar Alhamis, biyo bayan wata motar Bas da ta kama da wuta a kan hanyar Bulawayo zuwa Beitbridge dake kudancin kasar. Akalla wasu mutane 20 dake cikin motar ne suka ji raunuka.

Hatsarin shi ne mafi muni na biyu, da aka yi a Zimbabwe cikin kasa da makonni biyu, bayan na ranar Larabar makon da ya gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 50 a wata motar bas, a kusa da babbar hanyar Harare zuwa Mutare.

Motar da ta yi hatsarin ranar Alhamis ta fito ne daga Zvishavane dake lardin Midlands, inda ta doshi Musina dake Afrika ta Kudu.

Shugaba Mnangagwa ya ce hatsarin ya nuna karuwar barazanar da ake fuskanta a kan titunan kasar dake bukatar daukin gaggawa.

Ya ce hatsarin na baya-bayan nan, ya sa dole kasar ta tsaya ta sake duba dokokin tuki tare da yadda ake kiyaye su, domin kare daukar abubuwan da ba su kamata ba cikin motocin haya da mutane ke hawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China