in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 47 sun mutu a wani mummunan hadarin mota a Zimbabwe
2018-11-08 10:19:12 cri
A kalla mutane 47 ne suka mutu a sanadiyyar wani mummunan hadari a kasar Zimbabwe da yammacin jiya Laraba bayan da wasu motocin bus guda biyu suka yi karo da juna.

Kakakin hukumar 'yan sanda Paul Nyathi ya shedawa kamfanin dillancin labaran Xinhua cewa, hadarin ya faru ne a kusa da garin Rusape dake lardin Manicaland, mai tazarar kilomita 156 daga Harare, babban birnin kasar.

Nyathi ya ce, mutane 47 ne aka tabbatar da mutuwarsu, sai dai kawo yanzu ba'a gano musabbin hadarin ba.

Daga cikin mutanen 47 da suka mutu, 45 manya ne, sai kananan yara 2, in ji Nyathi.

Manyan motocin biyu mallakin kamfanonin Bolt Cutter da Smart Express ne, suna daga cikin kamfanonin sufuri biyu masu tafiyar nisan zango na cikin gida a kasar.

Nyathi ya ce, har yanzu jami'an 'yan sanda suna ci gaba da aiki a inda lamari ya faru, kuma ana sa ran adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China