in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka mutu a hadarin motocin Bas a Zimbabwe ya karu zuwa 50
2018-11-09 21:10:44 cri

Rahotanni daga kasar Zimbabwe na cewa, yawan mutanen da suka mutu sanadiyyar taho mu gama da wasu motocin bas biyu suka yi a kasar ranar Laraba a kan babbar hanyar Harare-Mutareya ya karu zuwa 50, baya ga wasu mutane 80 da suka ji rauni.

Tuni dai gwamnati ta ayyana hadarin a matsayi wani bali'i da ya afkawa kasar. A halin da ake ciki kuma, 'yan sanda sun fara farautar direba da yaron daya daga cikin motocin bas din da suka yi hadari, bayan da suka arce daga wurin da hadarin ya faru.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China