in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Rasha da Indiya sun amince su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu
2018-12-01 16:36:39 cri
Shugabannin Sin da Rasha da India, sun yi tattaunawa mai zurfi tare da musayar, game da hadin gwiwar dake tsakanin kasashensu karkashin sabon yanayin da ake ciki.

Yayin tattaunawar da suka yi a jiya, shugaban Sin Xi Jinping da na Rasha Vladimir Putin da Firaministan India Narendra Modi, sun amince su karfafa tare da kara hadin gwiwa da ke tsakaninsu da kuma cimma matsaya guda, da nufin inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban duniya.

Shugaba Xi ya yi bayanin cewa, Sin da Rasha da India, manyan kasashe ne da ke da muhimmin tasiri, kana su kasance muhimman abokan huldar juna.

A cewarsa, kasashen 3, suna da muradu da burika iri daya, sannan suna da hakkin samar da makoma mai kyau ga yankinsu da ma duniya baki daya.

Har ila yau, ya ce samun ci gaba na bai daya da alakar kut da kut dake tsakanin Sin da Rasha da India karkashin yanayin da ake ciki, ya zama muhimmin jigo ga samun zaman lafiya da tabbas, yayin da duniya ke fuskantar sauye-sauye. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China