in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya bukaci kungiyar G20 ta tafiyar da tattalin arzikin duniya yadda ya kamata
2018-12-01 15:50:39 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci kungiyar G20, ta rungumi tsarin bude kofa da hadin gwiwa da kirkire kirkire da tafiya tare da dukkan bangarori da kuma tafiyar da tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.

Xi Jinping ya yi wannan kira ne a jiya, lokacin da yake jawabi ga taron kungiyar G20 karo na 13 a birnin Buenos Aires na Argentina.

Ya kuma gargadi shugabannin kasashen kungiyar game da yadda kalubale ke gaggauta karuwa cikin tsarin tattalin arzikin duniya, inda ya lashi takobin kasar Sin za ta jajirce wajen shiga wani sabon zagaye na aiwatar da gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga waje, tare da inganta kokarin kare hakkokin mallakar fasaha da kara shigo da kayayyaki.

Shugaba Xi wanda ya yi waiwaye, yana mai cewa shekaru 10 ke nan tun bayan da rikicin hada-hadar kudi ya barke a duniya, inda aka kira taron G20 na farko, ya ce yayin da tattalin arzikin duniya a yanzu ke samun ingantuwa, har yanzu ba zai iya kaucewa tasirin rikicin ba.

Har ila yau, shugaba Xi Jinping, ya ce dole ne a matsayinsu na mambobin G20, su bi tafarkin tarihi domin tsara makoma ta gaba. Yana mai cewa, yayin da dan Adam ke fafutukar neman ci gaba da cimma nasarori ba tare da yin kasa a gwiwa ba, bude kofa da hadin kai tsakanin kasashe abu ne da ba za a iya dakatarwa ba, duk da kalubalen dake tattare da tattalin arzikin duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China