in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)Shugaban Kasar Sin ya fara ziyarar aiki a Argentina tare da halartar taron G20
2018-11-30 10:50:56 cri
A jiya Alhamis ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya isa Buenos Aires, babban birnin kasar Argentina don fara ziyarar aiki a kasar, inda kuma zai halarci taron kolin kungiyar G20 karo na 13.

A madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta, shugaba Xi Jinping ya isar da gaisuwa ga jama'ar kasar Argentina. Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin da Argentina kawaye ne da ke amincewa da juna da samun moriyar juna. Kasashen biyu sun nuna goyon baya ga juna wajen samun ci gaba, da zurfafa hadin gwiwarsu da sada zumunta da juna, da hada kai a harkokin kasa da kasa da yankuna.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Argentina ita ce kasar farko a nahiyar kudancin Amurka da ta karbi bakuncin taron koli na kungiyar G20, kana bana shekaru 10 ke nan da fara gudanar da taron kolin, don haka taron yana da ma'ana matuka. Shugaba Xi yana fatan hada kai tare da bangarori daban daban ciki har da kasar Argentina wajen yin hadin gwiwa da juna kamar cikin jirgin ruwa daya, da kokarin raya tattalin arzikin duniya, kamar babban jirgin ruwan tattalin arzikin duniya ne ya sake tashi daga kogin La Plata zuwa babban teku. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China