in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya bayyana muhimmancin huldar kasa da kasa ga Sakatare Janar na MDD
2018-12-01 16:32:58 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce har kullum, kasarsa na ammana cewa, huldar kasa da kasa ita ce hanya daya tilo da ta fi dacewa da moriyar jama'ar duniya baki daya.

Xi Jinping ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da yake ganawa da Sakatare Janar na MDD a gafen taron G20 dake gudana a birnin Buenos Aires na Argentina.

Ya kara da cewa, kasashen duniya ba su da wani zabi mafi kyau da ya wuce karfafa hulda da hadin gwiwa a tsakaninsu, domin tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta daya bayan daya.

Shugaban na kasar Sin, ya ce ya dade yana nazarin yadda kasashen duniya za su cimma hadin gwiwa da samun kwanciyar hankali da hadin gwiwa irin ta moriyar juna yayin da ake da muradu da matsaloli mabanbanta, al'amarin da ya kai shi ga gabatar da kudurinsa na gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama da kuma shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China