in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen BRICS sun amince su daukaka tsarin huldar kasa da kasa
2018-12-01 15:54:47 cri
Shugabannin kasashe masu samun saurin bunkasar tattalin arziki wato BRICS, sun cimma gagarumar matsaya a jiya Juma'a a gefen taron G20, inda suka amince da daukaka tsarin huldar kasa da kasa bisa kiyaye dokokin da aka gindaya.

Yayin wani taro da ya gudana karkashin jagorantar shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, wanda a yanzu ke rike da kujerar shugabancin kungiyar na karba-karba, shugabannin kasashen sun yi musayar ra'ayi game da yanayin tattalin arzikin duniya da kalubalen da yake fuskanta da kuma hadin gwiwar dake tsakaninsu karkashin kungiyar BRICS.

Shugabannin kasashe mambobin kungiyar da suka hada da Xi Jinping na Sin da Michel Temer na Brazil da Vladimir Putin na Rasha da Firaministan India Narendra Modi ne suka halarci taron.

Da yake jawabi, shugaba Xi Jinping, ya ce ya kamata kasashen BRICS su inganta hadin kai da bin tafarkin da ya dace, da karfafa tattaunawa a tsakaninsu, sannan su nuna sanin ya kamata, tare da yin aiki tare, domin kiyaye huldar kasa da kasa bisa hanyar da ta dace ta yadda za a inganta zaman lafiya da ci gaban duniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China