Ministocin raya al'adu na kasashen BRICS sun sanya hannu kan yarjejeniyar ne a Johannesburg, bayan shafe watanni suna tuntubar juna. Yarjejeniyar zata tabbatar da kasashen 5 sun karfafa hadin gwiwarsu a bangaren raya al'adu, da fannin ado da kwalliya. Ministan al'adu na kasar Afrika ta kudu Nathi Mthethwa ya bukaci a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar.
Ministocin raya al'adun sun amince zasu shigar da sabon bankin raya cigaba domin samar da kudaden da za'a yi amfani dasu wajen ayyukan raya al'adu da ayyukan fasahar gargajiya. Sannan sun amince da kafa kwamitin aikin raya al'adu na BRICS wanda zai kunshi manyan jami'ai daga kasashen na BRICS, domin bunkasa mu'amala tsakanin mutum da mutum da karfafa hadin gwiwar kamfanoni fasahar kirkire kirkire.
Mataimakin ministan raya al'adu da yawon shakatawa na kasar Sin Xiang Zhaolun ya bayyana cewa, al'adu wani muhimmin bangare ne a hadin gwiwar BRICS. Zai kara samar da fahimtar juna a tsakanin mambobin kasashen BRICS, kuma zai inganta bangaren yawon bude ido da kawo babbar moriya ga tattalin arziki. Ministocin sun kuma amince da kafa wani tsari na hadin gwiwa tsakanin cibiyoyi. (Ahmad)