Shugabannin na BRICS sun sanar da hakan ne cikin sanarwar bayan taron kolin kungiyar karo na 10 da ya gudana a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu. A cikin sanarwar, shugabannin sun bayyana muhimmancin gina muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a da hade nahiyar Afirka, sun kuma yaba da irin managartan matakan da kungiyar tarayyar Afirka ke dauka na gano da kuma magance kalubalen kayayyakin more rayuwa da nahiyar ke fuskanta, ta hanyar sabon shirin hadin gwiwa na raya nahiyar da kuma shirin samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a Afirka.
Bugu da kari, shugabannin sun bayyana muhimmancin zuba jari a bangaren kayayyakin more rayuwa bisa moriyar juna, a wani mataki na taimakawa ci gaban masana'antu da samar da guraben ayyukan yi,koyar da sa'ao'i,samar da abinci mai gina jiki, tsaro, kawar da talauci da samar da ci gaba mai dorewa a Afirka. (Ibrahim Yaya)