Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin da jama'arta suna goyon bayan kasashen Afirka da jama'arsu da su yi kokarin neman samun zaman lafiya da wadata da ci gaba. Kasar Sin ta shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD a nahiyar Afirka. Kana kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasashen Afirka kan yadda za su inganta karfinsu na kiyaye zaman lafiya da taimaka musu wajen warware matsalolin da yankin ke fuskanta cikin hanzari. (Zainab)