Rahotanni da hukumar kiyaye tsaro ta kasar Rasha da hukumar kula da kan iyaka ta kasar Crimea suka fitar sun nuna cewa, a ranar 25 ga wata, jiragen ruwan sojojin ruwa na kasar Ukraine guda biyar sun yi yunkurin ratsa zirin Kerch ba tare da samun iznin kasar Rasha ba, kasar Rasha ta dauki wasu matakai don hana jiragen ruwan kasar Ukraine shiga yankin ruwan.
Wani rahoto da ma'aikatar watsa labarun kasar Ukraine ta bayar, na cewa, jiragen ruwan yaki biyu da wani jirgin ruwan sojojin ruwan kasar Ukraine sun yi yunkurin ratsa zirin Kerch a kokarin shiga tekun Bahar Asuwad ta tekun Azov a ranar 25 ga wata. Wani jirgin ruwan yaki na kasar Rasha ya ci karo da jirgin ruwan sojojin ruwan Ukraine, tare da kai hari ga wani jirgin yaki na kasar Ukraine, lamarin da ya haddasa raunatar mutane 6. Daga bisani Rasha ta kama jiragen ruwan kasar Ukraine guda uku.
Bayan faruwar lamarin, Rasha da Ukraine sun dauki wasu matakai, hakan ya sa aka samu tsanantar halin da ake ciki a tsakaninsu. (Zainab)