in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya yi tir da harin da aka kai wa ofishin jakadancin kasar Sin a Pakistan
2018-11-25 15:45:50 cri
Kwamitin sulhu na MDD, ya yi tir da kakkausar murya, kan harin da aka kai wa karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Karachi da kuma wanda aka kai wata kasuwa a lardin Khyber Pakhtunkhwa, dukkansu a kasar Pakistan.

Kwamitin ya yabawa martanin gaggawa da hukumomin Pakistan suka mayar, yana mai bayyana jimami da jaje ga iyalan wadanda hare-haren ya rutsa da su da kuma gwamnatin Pakistan, sannan ya yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Mambobin kwamitin sun kuma jadadda muhimmiyar ka'idar girmama ofisoshin jakadanci da na diflomasiyya, da kuma nauyin da yake kan kasashen da ofisoshin suke na daukar dukkan matakan da suka dace na kare ofisoshin diflomasiyya daga kutse ko barna, da kuma kare duk wani tarnaki ga kwanciyar hankalin ofisoshin da martabarsu.

Har ila yau, sun jadadda bukatar cafke wadanda suke da hannu da masu samar musu da kudi da masu kitsawa da daukar nauyin ayyukan ta'addanci don tabbatar da hukunta su, suna masu bukatar kasashe su hada hannu da gwamnatin Pakistan da dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki.

Mutane 4 ciki har 'yan sanda 2 aka kashe a harin da aka kai karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake kudancin birnin Karachi na Pakistan. An kashe maharan kafin su kai ga kutsawa harabar ofishin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China