in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD kan gabas ta tsakiya ya yi kira da sulhu tsakanin bangarorin Falasdinu
2018-11-20 10:55:38 cri
Wakilin MDD game da batun zaman lafiya a Yankin gabas ta tsakiya Nickolay Mladenov, ya bukaci a gaggauta sulhunta bangarorin Falasdinu, biyo bayan sabon rikicin da ya barke a Gaza.

Da yake jawabi kwamitin sulhu na MDD, Nickolay Mladenov, ya yi kira da kada bangarorin su bata lokaci, yana mai bukatar su hau teburin sulhu domin cimma kwakkwaran sakamako cikin watannin 6 masu zuwa.

Ya ce batun sulhunta bangarorin Falasdinu zai amfanawa al'ummar Falasdinu, kana zai samar da zaman lafiya. Ya ce nasarar kokarin al'ummomin kasa da kasa, ya dogara ne kan kudurin bangarorin na shawo kan matsaloli da jure abun da siyasar cikin gida zai haifar da kuma tsayawa kan shirin samar da sulhu mai dorewa.

Ya ce dole ne bangarorin su yi amfani da damar yunkurin da Masar ke jagoranta, na mayar da gaza karkashin ikon halaltacciyar gwamnatin Falasdinu.

Har ila yau, ya ce al'ummar Falasdinu na neman shugabancinsu ya hade Gaza dake hannun kungiyar Hamas da yammacin kogin Jordan dake karkashin hukumar Falesdinu, da cimma burin kawo karshen mamayar Isra'ila cikin lumana tare da kafa kasar Falasdinu karkashin kudurorin MDD. Yana mai cewa wannan shi ne muradin Falasdinawa, kuma shi ya dace da su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China