in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jarin da aka zuba a Najeriya a fasahar sadarwa ta zamani ya kai dala biliyan 70
2017-09-28 09:12:04 cri

Wasu alkaluman da gwamnatin Najeriya ta fitar a ranar Laraba ya nuna cewa, hannun jarin da aka zuba a kasar a fannin fasahar sadarwa ta zamani ya kai dalar Amurka biliyan 70.

An samu gagarumin ci gaba idan aka kwatanta da jarin dala miliyan 50 da aka zuba a kasar a shekarar 2001 a lokacin da aka baiwa kamfanonin wayar hannu lasisin gudanar da ayyukansu a karon farko a kasar ta yammacin Afrika.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da shugaban hukumar sadarwa ta Najeriyar NCC farfesa Umar Dambatta, ya rattabawa hannu.

Sanarwa ta ce, mafi yawan hannayen jarin da aka zuba na kasashen waje ne.

A halin yanzu kasar na da kashi 21 bisa 100 na karfin sadarwa, kana kasar na yunkurin kara hanyoyin zuba jari a fannin sadarwar.

A cewar sanarwar, Najeriya tana kokarin samar da kashi 30 bisa 100 na karfin sadarwar nan da shekarar 2018.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China