in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana sun yi kira da a kara zuba jari don farfado da fasahar kere-kere a Afirka
2018-02-15 12:28:08 cri

Masana a fannin fasahar kere-kere daga nahiyar Afirka da sauran sassan duniya, sun yi kira da a kara zuba jari a bangaren watsa labarai da fasahar sadarwa ta zamani(ITC) a nahiyar, a wani mataki na hanzarta farfado da fasahar sadarwar zamani a nahiyar ta Afirka.

Masanan sun yi wannan kiran yayin taron kolin fasahar sadarwa na Afirka da aka bude jiya Laraba a birnin Kigalin kasar Rwanda. Manufar taron wanda za a rufe a yau Alhamis, ita ce zakulo sabbin fasahohi na zamani.

A nasa jawabin manaja mai kula da dabarun hadin gwiwar kayayyaki a kamfanin Facebook Proud Dzambukira, ya ce nahiyar Afirka na daya daga cikin muhimman wurare dake da damammaki na zuba jari da harkokin kasuwanci, amma kuma jarin da ake zubawa a fannin fasahar sadarwa ta zamani kalilan ne, lamarin da ke kawo cikas ga ci gaban wannan sashe. Muddin ana bukatar ganin nahiyar ta samu bunkasa a fannin fasahar sadarwa ta zamani a duniya, wajibi ne a kara zuba jari a wannan bangaren cikin shekaru 10 masu zuwa.

Ya kara da cewa, an samu ingantuwar kayayyakin more rayuwa a nahiyar cikin 'yan shekarun nan, inda aka gina sabbin hanyoyin mota, da filayen jiragen sama, tashoshin samar da wutar lantarki da kafofin sadarwa. A don haka ya kamata wannan ya karfafawa masu sha'awar zuba jari gwiwar kara zuba jari a bangaren fasahar sadarwa ta zamani.

Kimanin shugabanni da masana a fannnin fasahar kere-kere daga nahiyar Afirka da kasashen duniya 250 ne suka halarci wannan taro.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China