in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar sadarwa ta Nijeriya da kamfanin Sin sun fara gudanar da shirin "yara manyan gobe"
2017-09-10 13:14:07 cri
A ranar 7 ga wata ne, ma'aikatar sadarwa ta Nijeriya tare da hadin gwiwar kamfanin Huawei na kasar Sin suka shirya wani bikin na fara shirin ba da hora mai taken "Yara manyan gobe", watau "Seeds for the future" a turance.

Wakilai daga tawagar dalibai 10 ne suka halarci wannan biki, wadanda suka bar Najeriya zuwa nan kasar Sin a jiya Asabar domin halartar shirin na tsawon makwanni guda biyu.

A yayin bikin, ministan harkokin sadarwa na kasar Nijeriya Abdur Raheem Adebayo Shirru ya bayyana cewa, cikin shekarun baya bayan nan, kamfanin Huawei ya dukufa wajen samar da muhimman na'urori da fasahohin sadarwa na zamani, sabunta fasahohin da abin ya shafa da kuma samar da ilmi game da fasahohin sadarwa na zamani ICT, lamarin da ya ba da gudummawa kwarai da gaske ga bunkasuwar zaman takewar al'umma a Nijeriya. Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi godiya matuka ga kamfanin Huawei bisa ga babbar gudummawar da ya bayar, a sa'i daya kuma, tana son ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kamfanin Huawei domin yin kwaskwarima ga tsarin tattalin arziki ta hanyoyin zamani.

Bugu da kari, ya yiwa daliban da suka tafi kasar Sin domin neman ilmi fatan alheri. Ya ce, yana fatan za su yi amfani da wannan dama mai kyau wajen karfafa kyakkyawan zumunci dake tsakanin kasashen Sin da Nijeriya.

Cikin wadannan makwani biyu, ana sa ran daliban goma za su ziyarci hedkwatar kamfanin Huawei dake birnin Shenzhen na kasar Sin, inda za a nuna musu sabbin na'urori da fasahohin sadarwa na zamani, haka kuma, za su sami damar yin mu'amala da manyan masana a wannan fanni, ta yadda za su kara saninsu game da al'adun kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China