Masana da masu tsara manufofi dake ganawa a birnin Nairobin Kasar Kenya gabanin taron kolin kungiyar sadarwa ta duniya da zai gudana a kasar Dubai cikin watan Oktoba, sun bayyana cewa, akwai bukatar cimma matsaya domin hanzarta raya harkokin masana'antun nahiyar ta hanyar amfani da fasahohin kere-kere da kirkire-kirkire.
Babban sakararen fasahar ICT a fadar shugaban kasar Kenya Joe Mucheru ya jaddada cewa, hade manufofi da tsare-tsare sune za su tabbatar da cin gajiyar fasahohin zamani daidai wa daidaida a nahiyar ta Afirka.
Haka kuma, ana fatan idan har aka yi magana da murya guda, kasashen na Afirka za su samu saukin cin gajiyar dake tattare da ci gaban fasahar ta ICT a duniya. (Ibrahim)