Asusun da aka kaddamar a baya-bayan nan tare da wasu shirye-shirye, sun ta'allaka ne kan manyan batutuwa 3, da suka hada da rungumar shirye shiryen sulhu da matakan kare barkewar rikici da inganta ayyukan kungiyar da kuma taimakawa ayyukan wanzar da zaman lafiya.
Asusun na wanzar da zaman lafiya a nahiyar, wanda tuni aka kafa masa kwamitin amintattu mai mabobi 5 da kuma jagoransu, zai fara aiki ne da kudi dala miliyan 100.
Shugaban Rwanda kuma shugaban Tarayyar mai ci wato Paul Kagame, ya bayyana yayin bikin kaddamar da asusun a ranar Asabar cewa, asusun zai yi aiki ne wajen tabbatar da zaman lafiya da shawo kan kalubalen tsaro bisa matakan nahiyar. (Fa'iza Mustapha)