in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaiministan Libya ya nuna cikakken goyon bayansa na dunkulewar rundunar sojojin kasar
2018-10-23 09:50:46 cri
Firaiministan kasar Libya dake samun goyon bayan MDD Fayez Serraj, ya bayyana cikakken goyon bayansa a yunkurin da ake na cimma daidaito game da dunkulewar rundunar sojin kasar.

A ta bakin kakakinsa Mohamed al-Sallak wanda ya bayyanawa taron maneman labarai a Tripoli babban birnin kasar Libyan, ya ce "Firaiminitan yana ci gaba da bibiyar wannan muhimmin batu na cimma matsaya tare da jami'an rundunar sojojin kasar".

Serraj, ya nanata bukatar cimma matsaya ta karshe domin kafa dunkulalliyar rundunar sojojin kasar, a halin yanzu, ana bukatar samun cikkaken bayani game da matsayin hukumar fararen hula, da suka hada da babban kwamandar koli na rudnunar sojoji da kuma mukarrabansa.

Serraj ya tabbatar da cewa, mayar da hukumar gudanarwar sojojin kasar kwaya daya tilo wani muhimmin al'amari ne da zai taimaka wajen kawo karshen rikicin siyasar kasar, in ji kakakin.

Tun a watan Oktoban shekarar 2017, babban birnin kasar Masar wato Cairo ya karbi bakuncin tarurrukan jami'an sojojin kasar Libyan da nufin tattauna batun dunkulewar rundunar sojojin kasar ta Libya.

Tun bayan tashin hankalin shekarar 2011 wanda ya yi sanadiyyar hambarar da gwamnatin shugaban kasar Muammar Gaddafi, Libya take ci gaba da fuskantar tashe tashen hankula da tabarbarewar tsaro da kuma rarrabuwan kawuna tsakanin bangarorin siyasar kasar, lamarin da ya haifar da raba hukumomin shiyyoyin gabashi da yammacin kasar, wanda ya hada har da rundunar sojojin kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China