Tauraron dan-Adam din shi ne na 32 a tsarin na Beidou, kana daya daga rukunin tsarin taurarin dan-Adam na Beiduou- mai lamba 2. Kaddamar da tauraron dan-Adam din shi ne na 280 da aka yi amfani da rokar Long March wajen harba su.
Tun a shekarar 2017 ne kasar Sin ta fara kera rukuni na 3 na tsarin na Beidou, kuma yanzu haka an harba rukunin taurarin dan-Adam guda 8 na tsarin Beidou mai lamba 3 zuwa sararin samaniya. (Ibrahim)