in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta iya yin mu'amala da kasashen duniya kan fasahohin yin kwaskwarima, in ji Ban Ki-moon
2018-11-25 16:36:45 cri
Shugaban majalisar zartaswa ta dandalin Boao na yankin Asiya, kana tsohon Sakatare Janar na MDD Ban Ki-moon, ya ce kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba, tun bayan da ta fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje a shekarar 1978 zuwa yanzu.

Ban Ki-Moon, wanda ya bayyana haka a birnin Seoul, fadar mulkin kasar Koriya ta Kudu, ya ce a ganinsa, kasar Sin za ta iya yin mu'amala da sauran kasashen duniya kan fasahohinta na neman ci gaba.

Ya ce a shekarar 1978, ma'aunin tattalin arziki na GDP na kasar Sin bai kai 2% na karfin tattalin arzikin duniya ba, amma a halin yanzu, kasar Sin ta zama kasa ta biyu mai karfin tattalin arziki a duniya.

Ban Ki-moon ya ce, kasar Sin ta sami matukar ci gaba cikin wadannan shekarun da suka gabata, kuma ya dace ta gabatar da fasahohinta na neman ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma ga sauran kasashen duniya.

Bugu da kari, ya ce, bisa labarin da MDD ta fitar, adadin mutane masu fama da tsananin talauci ya ragu daga biliyan 1.9 na shekarar 1990 zuwa miliyan 836 a shekarar 2015, lamarin da ya nuna cewa, an cimma burin MDD na kawar da tsananin talauci da aka tsara a shekarar 2000. Har ila yau, ya ce kasar Sin ta ba da babbar gudummawa wajen kawar da tsananin talauci cikin shekaru 40 da suka gabata, wato bayan fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga waje, inda ya ce ana iya cewa, kasar Sin ta bada gudunmuwa sosai ga muhimmin burin MDD, na kawar da kangin talauci.

Haka zalika ya ce, a halin yanzu, kasar Sin ta dukufa wajen cimma burinta na kawar da kangin talauci tun daga tushe kawo zuwa shekarar 2020, lamarin da zai kasance babbar nasara ga kasar, wanda ke da muhimmiyar ma'ana gare ta, da ma duniya baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China