in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta gina bututun karkashin teku mai dauke da layin dogo
2018-11-23 10:20:14 cri
Mahukuntan kasar Sin, sun tabbatar da shirin gina wani bututun karkashin kasa na musamman, wanda zai kunshi layin dogo na zamani, domin jiragen kasa masu saurin tafiya.

An dai tsara gina wannan bututu ne a lardin Zhejiang dake gabashin kasar. Zai kuma hade birnin Ningbo da birnin Zhoushan dake gabashin Zhejiang. Aikin zai kunshi kilomita 70.92, ciki hadda bututun karkashin teku mai tsayin kilomita 16.2.

Jiragen kasa samu gudun kilomita 250 a ko wace sa'a, za su rika sufuri a cikin bututun da zarar aikin ya kammala, wanda hakan zai rage tsayin tafiya tsakanin biranen biyu, daga sa'a daya da rabi zuwa kasa da mintuna 30.

Sin na da layin dogo mai saurin tafiya da tsayin sa ya kai kilomita 25,000, adadin da zarta sama da kaso 60 bisa dari, na daukacin tsayin layukan dogon da ake da su a duniya baki daya. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China