Ya ce Sin da Gambia, na hadin gwiwa a sassa masu tarin yawa, kuma abun farin ciki ne, ganin yadda ake ci gaba da raya hadin kai, da samar da karin ayyuka tsakanin kasashen. Jami'in ya ce hanyoyin mota, da gadoji, wadanda kasar Sin ta tallafa wajen ginawa a kasar, kuma ake fatan kaddamarwa cikin wata mai zuwa, misali ne na irin gajiyar da hadin gwiwar ya haifar.
Kaza lika a cewar sa, tsare tsaren nan guda 8 na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka karkashin dandalin FOCAC, sun dace da manufofin raya kasa na gwamnatin Gambia.
Daga nan sai Mr. Ma ya bayyana shigar kasar Gambia dandalin FOCAC, a matsayin matakin shiga babban iyalin wannan dandali, kuma a cewar sa ko shakka babu, Gambia za ta ci gajiya maras iyaka daga sakamakon taron dandalin da ya gudana a birnin Beijing. (Saminu Alhassan)