in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sana'ar ba da hidima ta fannin harsuna tana bunkasa da sauri cikin shekaru 40 da suka gabata
2018-11-20 10:56:55 cri
Jiya Litinin, kungiyar masu fassara ta kasar Sin ta fidda rahoton bunkasuwar sana'ar ba da hidima ta fannin harsuna na shekarar 2018, inda ta nuna cewa, sana'ar ba da hidima ta fannin harsuna, musamman ma a fannin fassarawa ta sami ci gaba kwarai cikin shekaru 40 da suka gabata, a yayin da kasar Sin take aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga waje. Lamarin da ya ba da gudummawa matuka ga kara mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen waje.

Ya zuwa karshen watan Yuni na shekarar bana, gaba daya akwai kamfanonin ba da hidima a fannin harsuna guda 9652, adadin da ya karu da saurin gaske.

A jiya kuma, an gabatar da rumbun bayyanai game da "yadda za a fassara muhimman kalmomin siyasa daga Sinanci zuwa harsunan waje". Hukumar harsunan waje ta kasar Sin ta tsara wannan littafi, wanda ya kasance rumbun bayyanai na farko da kasar Sin ta fidda, kan yadda za a fassara wasu muhimman kalmomin siyasa daga Sinanci zuwa harsunan waje. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China