in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda na kokarin kawo karshen bautar da yara ta hanyar gindaya hukunci mai tsauri
2018-03-06 10:13:59 cri
Gwamnatin Rwanda na duba yiwuwar daukar tsauraran matakan da za su yi tasiri wajen magance matsalar bautar da yara a kasar.

Da yake bayani game da dokar daidaita harkokin kwadago a majalisar dokokin kasar, ministan kwadago na kasar Fanfan Rwanyindo ya ce masu bautar da yara za su fuskanci tsatssauarn hukunci .

A cewar ma'aikatar kwadago ta kasar, shekara 16, ita ce shekara mafi karanci ta fara kwadago.

Fanfan Rwanyindo ya ce ana tilastawa yara kanana masu shekaru 10 shafe lokaci mai tsawo suna aiki a bangarorin noma da hakar ma'adinai da gine-gine, galibi a karkashin yanayi mara kyau kuma ba tare da samun kiwon lafiya ba.

A cewar wani bincike da hukumar kididdiga ta kasar ta yi a shekarar 2015, kaso 2.1 na yara a kasar na ayyukan dake tattare da hatsari.

Bayanai daga ma'aikatar kula da iyali ta kasar na nuni da cewa, sama da yara 11,000 ne aka janye daga ayyukan bauta a cikin shekaru 5 da suka gabata.

A nata bangaren, shugabar majalisar dokokin kasar Donatille Mukabalisa, ta ce samarwa iyalai matalauta hanyoyin samun kudin shiga zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen bautar da yara tunda talauci ne ke sanya galibin yaran fara ayyukan bauta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China