in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ai da masanan Senegal sun yi ta tsokaci game da ziyarar shugaba Xi
2018-07-23 11:05:32 cri

Bangarori daban daban na kasar Senegal sun yi ta sharhi game da ziyarar aikin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar ta yammacin Afrika bayan da ya karkare ziyarar aikin a jiya Lahadi.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Senegal ya jiyo shugaban kasar Senegal Macky Sall yana bayyana cewa, kasar Sin ta kasance sahihiyar kasa kuma muhimmiyar aminiya ga kasar Senegal.

Kalaman na mista Sall ya ci gaban da cewa, kasar Sin kasance mai dadadden tarihi na wayewar kai wadda take da tarihin dubban shekaru, tana da dunbun arziki, da tarihi mai kayatarwa, kuma ta kasance kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya wadda tsarin ci gabanta ya kasance abin koyi ga sauran kasashe masu tasowa.

Tsohuwar firaiministar kasar Senegal Aminata Toure ta fada cikin wata hira da kafafen yada labaran kasar cewa, tana sa ran ziyarar Xi za ta kara bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da musayar al'adu tsakanin kasashen biyu karkashin tsarin moriyar juna.

Kader Diop, wani kwararren masani a sashen koyon aikin jarida na jami'ar Dakar, ya ce, ziyarar shugaba Xi ta kara tabbatar da kyakkyawar hadin gwiwar dake tsakanin Senegal da Sin.

Taimakon da kasar Sin ke baiwa Afrika bai takaita ga wata kasa daya tilo ba, sai dai ya kara nuna yadda Afrika ke samun bunkasuwa bisa kyakkyawar hulda dake tsakanin Sin da kasashen Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China