Wakilin na Sin ya yi wannan kiran ne yayin zaman kwamitin sulhun MDD game da kasar ta Iraki, Yana mai cewa, ya kamata gwamnatin Iraki ta hanzarta aiwatar da shirinta na sake gina kasar, da ba da muhimmanci ga bangaren albartakun kasar, da bunkasa tattalin arziki da karfafa samar da horo ga ma'aikata da ma inganta rayuwar al'ummar kasar.
Jami'in ya kuma bukaci al'ummomin kasa da kasa da su baiwa kasar ta Iraki duk wani taimako da goyon baya da take bukata, da sassauta yanayin jin kai da kasar ke ciki, da taimakawa kasar a kokarin da take na farfado da tattalin arziki, da samar da yanayin da ya dace na sake gina kasar.
Ma ya kuma bayyana kudurin kasar Sin na goyon bayan duk wani mataki da ya dace na daidaita harkokin siyasar kasar da yaki da ta'addanci. Haka kuma, kasar Sin za ta shiga a dama da ita wajen sake gina tattalin arzikin kasar ta Iraki, za kuma ta ci gaba da taimakawa Irakin bisa karfinta. (Ibrahim)