in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira ga kasa da kasa su yi kokarin farfado da tattaunawar sulhu tsakanin Isra'ila da Falasdinu
2018-11-20 09:43:44 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Ma Zhaoxu, ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa,su yi kokarin farfado da tattaunawar sulhu tsakanin Falasdinawa da Isra'ilawa.

Ma Zhaoxu, ya shaidawa kwamitin sulhu na MDD cewa, dole ne al'ummomin kasashen duniya da kwamitin, su gaggauta daukar nauyin kaddamar da sabon zagaye na kokarin inganta zaman lafiya tsakanin bangarorin 2.

Ya kara da cewa, ya kamata dukkan bangarorin dake da muhimmin tasiri, su taka rawar da ta dace wajen lalubo hanyoyin sulhu da kawo karshen takkadamar dake tsakaninsu.

Ya ce matakin kafa kasashe biyu, ita ce mafita ga rikicin, sannan ainihin matsayin birnin Kurdus muhimmin batu ne cikin aikin wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Bugu da kari, Ma Zhaoxu, ya ce kasar Sin ta kuduri niyyar inganta wanzar da zaman lafiya da kuma mara baya ga muradin al'ummar Falasdinu na dawo da halatattun hakkokinsu. Kuma kasar Sin na goyon bayan kafa kasa mai cikakkiyar 'yancin kai bisa iyakokin da aka shata a 1967, da kasancewar gabashin birnin Kudus matsayin babban birninta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China