in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya bukaci kawo karshen cin zarafin mata
2018-11-20 09:50:30 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bukaci a sauya tsaruka da al'adu domin kawo karshen cin zarafin mata.

Antonio Guterres ya bayyana haka ne yayin wani taro da aka yi don tunawa da ranar kawo karshen cin zarafin mata ta duniya, ta ranar 25 ga watan Nuwamban kowacce shekara.

Ya ce cin zarafin mata da 'yan mata annoba ce a duniya, inda ya ce ya samo asali ne daga gazawar maza na girmama daidaiton jinsi da martabar mata.

A wani yunkuri na kawo karshen cin zarafin mata ta hanyar lalata da musguna musu daga jami'an wanzar da zaman lafiya da ma'aikatan MDD, Antonio Guterres ya ce kusan kasashe mambobin majalisar 100 dake mara baya ga ayyukan majalisar na wanzar da zaman lafiya ne suka sa hannu kan wata yarjejeniyar sa kai, da nufin magance batun.

Baya ga haka, ya ce MDD na ci gaba kokarin samar da shirye-shirye domin taimakawa mata da 'yan mata, ta hannu asusun majalisar dake da nufin kawo karshen cin zarafin mata, wanda ya samar da sama da shirye shirye 460 a kasashe da yankuna 139 cikin shekaru 20 da suka gabata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China