in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya isa kasar Philippines domin fara ziyarar aiki
2018-11-20 13:40:50 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa kasar Philippines a yau Talata, domin fara ziyarar aiki irinta ta farko, da wani shugaban kasar Sin zai gudanar a kasar tun bayan shekaru 13 da suka gabata.

Kasar Philippines ce zangon karshe da shugaban zai ziyarta, a jerin kasashe 3 na yankin Asia da Fasifik da aka tsara zai ziyarta a wannan karo.

Tuni dai ya kammala ziyarar sa a Papua New Guinea, inda ya halarci taron shugabanni mambobin kungiyar hadin gwiwar raya tattalin arziki Asia da Fasifik karo 26, ya kuma ziyarci kasar Brunei. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China