in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Brunei sun yi alkawarin ciyar da alakar dake tsakaninsu zuwa gaba
2018-11-19 19:14:34 cri

A yau ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin dake ziyarar aiki a kasar Brunei ya gana da takwaransa na kasar Sultan Haji Hassanal Bolkiah, inda suka jaddada kudurinsu na karfafa alakar dake tsakanin kasashensu ta hanyar yin hadin gwiwa da kulla alaka a fannoni dabam-dabam

Shugabannin wadanda suka bayyana hakan cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar bayan ganawar tasu, sun kuma amince cewa, nasarar ziyarar shugaba Xi a kasar ta Brunei tana da muhimmanci wajen zurfafa alaka tsakanin sassan biyu.

Bugu da kari, shugabannin biyu sun amince su rika yin musaya tsakanin manyan jami'an kasashensu, da karfafa alaka bisa manyan tsare-tsare da dangantaka a tsakaninsu da yin musayar bayanai game da batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Sassan biyu za kuma su yi kyakkyawan amfani da alakar dake tsakaninsu a dukkan fannoni domin kara daidaita da ciyar da alakar dake tsakaninsu a fannoni dabam-dabam da kara karfafa hadin gwiwa a fannonin zuba jari da cinikayya.

Sassan biyu sun kuma bayyana gamsuwa game da ci gaban da suka samu a fannin alakar makamashi dake tsakaninsu, inda suka amince su ci gaba da taimakawa kamfanonin kasashen biyu da abin da ya shafa, ta yadda za su hada kai a fannonin albarkatun mai da iskar gas kan teku, bisa ka'idojojin kasa da kasa da akidar mutunta juna da nuna daidaito da samun moriya tare.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China