in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar EAC ta bukaci a yi al'ummar Afrika shaidar dan kasa ta amfani da na'urorin zamani
2018-11-20 11:03:00 cri
Hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD, ta yi kiyasin 'yan Afrika miliyan 500 ne ba su da shaidar dan kasa a hukumance, tana mai cewa rashin shaidar ta sa ba a tafiya da miliyoyin al'ummar nahiyar.

Sakatariyar zartarwar hukumar Vera Songwe ce ta bayyana haka yayin taron manyan jami'ai da aka yi ranar Lahadi a gefen taron AU na 11 da aka kammala a hedkatar tarayyar dake Addis Ababa na Habasha, inda ta bukaci shugabanni a Afrika su taimaka wajen yi wa al'umma shaida ta amfani da na'urorin zamani.

Taron da aka yi kan ajandar 2030 da 2063 dangane da samar da shaidar dan kasa ta na'urorin zamani, ya tattauna kan damarmaki da haddura da kuma darasin da irin shaidar ke dauke da su a kasuwar nahiyar Afrika.

Ta ce ingantaciyar shaida ga 'yan nahiyar zai tabbatar da kanana da matsakaitan sana'o'i wadanda suka mamaye kaso 80 na sana'o'in nahiyar, sun amafana.

A cewar hukumar ECA, yayin da kasashe kalilan suka samu ci gaba wajen samar da tsarin bada shaida ta na'ura, nahiyar baki daya, ba ta kai ga cimma moriyar dake tattare da tsarin ba.

Ba da shaidar ta na'urorin zamani zai saukakawa 'yan Afrika shiga harkokin tattalin arziki irin na zamani, wanda ake sa ran ya habaka a nahiyar zuwa sama da biliyan 300 ya zuwa 2025. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China