in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci EAC ta saukaka tsarukan cinikayya domin bunkasa bangaren masana'antu
2018-08-07 11:18:16 cri

Hukumar kula da tattalin arziki ta MDD (UNECA), ta bukaci kungiyar raya kasashen gabashin Afrika EAC, ta saukaka tsarukanta na cinikayya domin bunkasa ayyukan masana'antu.

Daraktan sashen raya ayyuka na hukumar Stephen Karingi, ya shaidawa Xinhua a birnin Nairobi cewa, bangaren masana'antu a yankin ba ya iya yin takara da na sauran yankuna kamar yadda ya kamata, saboda tsadar hidimomi da suka hada da inshora da kayayyakin aiki da kuma bangarorin hada-hadar kudi.

Stephen Karingi wanda ya bayyana hakan a gefen taron na 5 na kasuwar bai daya ta gabashi da kudanci Afrika, ya ce a bayyane yake cewa ana samun riba sosai idan aka bude kofa. Kuma kungiyar za ta cimma manufofinta na bunkasa ayyukan masana'antu idan za ta samu hidimomi masu rahusa daga saukaka tsarukanta na cinikayya.

Kasashe Mambobin kungiyar EAC, sun hada da Kenya da Uganda da Tanzania da Burundi da Rwanda da kuma Sudan ta kudu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China