Shugabannin kasashen Tanzaniya, Kenya, Uganda da Ruwanda na daga cikin wadanda suka halarci taron.
Shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli mai rike da shugabancin karba-karba na kungiyar ya sanar a taron cewar, kungiyar za ta shigar da kasar Sudan ta kudu don zama mambarta ta shida. Sudan ta kudu ta gabatar da bukatarta ta shiga kunigyar ne, bayan da ta samu 'yancin kanta a shekarar 2011, daga bisani kungiyar ta kafa wani kwamitin ministoci don yi mata bincike.
Ban da wannan kuma, saboda ganin mawuyancin hali da kasar Burundi ke ciki a halin yanzu, taron ya yanke shawarar dage wa'adin shugabancin kasar Tanzaniya zuwa shekarar 2017. Dadin dadawa, shugabanni masu halartar taron sun sanar da gabatar da sabuwar takardar iznin shiga gabashin Afrika ta yanar gizo don ingiza dunkulewar gabashin Afrika gaba daya. (Amina)