in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a fatattaki cutar shan inna baki daya daga nahiyar Afrika
2018-11-13 10:26:17 cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta yi kira da a hada karfi da karfe, wajen taimakawa nahiyar Afrika fatattakar cutar shan inna.

Babban wakilin hukumar a Kenya, Rudy Eggers, ya ce kasashen dake fadin nahiyar, na namijin kokari wajen ganin sun fatattaki cutar, a don haka suke bukatar taimako.

Yayin wani taron bitar ci gaban da aka samu na yaki da cutar a nahiyar, Rudy Eggers, ya ce dole ne a kawo karshen cutar ta hanyar yi wa kowanne yaro riga kafi, tare da kuma karfafa matakan sa ido.

Ya kara da cewa, dole ne a kawo karshen barkewar cutar ta hanyar tabbatar da yin dukkan allurar riga kafi da kuma gudanar da ingantattun gangamin wayar da kai.

Taron na yini 5, ya samu halartar manyan masu tsara manufofi da masana kiwon lafiya, daga yankin kudu da hamadar Sahara, domin bitar ci gaban da aka samu a kokarin da ake na fatattakar cutar shan inna.

Yayin taron, kasashe 7 ciki har da Kamaru da Nijeriya da Sudan ta Kudu da Afrika ta Kudu, za su mika rahoto game da kokarin da suke yi na kawar da cutar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China