Yayin taron shekara na hukumar MDD mai fafutukar wanzar da zaman lafiya a yankin Sahel, Amina Mohammed, ta ce idan ana son cimma zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, sannan a sauya daga bada agajin jin kai, zuwa ragewa da kawo karshen bukatun agajin jin kai, dole ne a magance matsalolin dake haifar da rikice- rikice daga tushe.
Ta kara da cewa, tushen wadannan matsaloli su ne nuna wariya da take hakkokin bil adama da rashin shugabanci na gari da rikici da tasirin sauyin yanayi a yankin.
Ta kara da cewa, dabara ta hadin gwiwa da za ta kunshi kowa da kowa, wadda gwamnatocin kasashen yankin za su samar, ita ce za ta taimakawa wajen samar da dawwaumamen zaman lafiya da ci gaba da ake tsananin bukata a yankin.
Har ila yau, Amin Mohammed, ta kara da bayyana kalubalen kudi da na yawan jama'a da yankin ke fuskanta, tana mai cewa jimilar abun da ake bukata na aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa a yankin, ta kai dala biliyan 140 a bana, wadda za ta rika karuwa kowacce shekara har ta kai dala biliyan 157 zuwa shekarar 2022. (Fa'iza Mustapha)