in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 300 sun jikkata sanadiyyar hatsarin jirgin kasa a Afrika ta kudu
2018-10-05 15:26:26 cri
A kalla mutane 300 ne suka jikkata sanadiyyar hatsarin jirgin kasa a garin Kempton Park na kasar Afrika ta kudu da yammacin jiya Alhamis.

Kakakin sashen kula da zirga-zirgar jiragen kasa a lardin Gauteng, Lillian Mofokeng ta ce fasinjoji sun samu raunaka amma ba masu tsanani sosai ba, inda ta ce an kai su asibitocin dake yankin.

A cewarta, wani jirgi da ya samu matsala ne ya karawa wani jirgi dake tsaye.

A nata bangaren, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasan fasinja ta kasar, ta ce za a gudanar da bincike don gano musababbin hatsarin, tana mai alkawarin yin aiki tare da sauran hukumomi domin nazarin lamarin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China