Sashen kula da makamashin kasar ne ya sanar a wannan makon cewa, farashin man fetur a kasar zai karu da kashi 99 bisa 100 wato daga Rand 1.24 a kan kowace lita tun daga yau Laraba. A wasu lardunan kasar masu ababen hawa za su dinga biyan Rand 17.08 a kan kowace litar man fetur.
Wannan shi ne karo na 7 da aka kara farashin mai a kasar cikin shekarar nan ta 2018. Sakamakon faduwar darajar kudin kasar Rand, da tashin farashin mai a kasuwannin duniya na daga cikin dalilan da suka haifar da kara farashin kudin man fetur din a Afrika ta kudu.
Wani masanin tattalin arziki na hukumar Efficient Group, Dawie Roodt, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Talata cewa, karin farashin man fetur na baya bayan nan zai haifarwa mafi yawan masu sayan kayayyaki a kasar raguwar kudaden shigarsu. (Ahmad Fagam)