in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta sha alwashin farfado da yaki da cutar malaria
2018-11-20 10:07:52 cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sha alwashin farfado da yakin da duniya ke yi da cutar zazzabin cizon sauro ko Malaria, bayan shafe shekaru ba tare da samun wani ci gaba na a zo a gani a yakin da ake yi da cutar ba.

WHO ta ce za ta aiwatar da wani gagarumin aiki tare da abokan huldarta a sassan duniya, domin baiwa kasashen da cutar ta fi kamari tallafi mafi dacewa da bukatun su, ciki hadda matakan kariya, da na magani, da zuba jari a fannin kandagarkin kamuwa da ita, tsakanin wadanda suke kan gaba wajen yiwuwar harbuwa da cutar.

Cikin rahoton hukumar na bana game da cutar ta malaria, WHO ta bayyana cewa, kiyasin mutanen da cutar ta kama a shekarar 2016 ya kai miliyan 217, yayin da a shekarar 2017 adadin ya haura zuwa miliyan 219. Alkaluman hukumar sun kuma nuna cewa, a shekarar 2015, adadin bai wuce miliyan 214 ba, yayin da na shekarar 2010 ya kai miliyan 239.

Har ila yau, a shekarar 2017, kimanin kaso 70 bisa dari na wadanda suke dauke da cutar su miliyan 151, ya kunshi mutum 274,000 da cutar ta hallaka, kuma mafi yawan su daga nahiyar Afirka da kasar India ne.

Domin tunkarar wannan kalubale, WHO da kawayen ta za su kaddamar da wani muhimmin tsari, na tallafawa kasashen da wannan cuta ta yiwa kamun kazar kuku.

Tsarin dai ya kunshi samar da kudade kai tsaye, domin tabbatar da nasarar sa. WHO ta ce domin cimma kudurinta na yaki da cutar nan da shekarar 2030, daga yanzu zuwa shekarar 2020, za a kashe kudaden da yawansu ya kai a kalla dala biliyan 6.6, sama da ninki guda na abun da ake kashewa a halin yanzu. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China