Ma Xiaowei, shugaban kwamitin lafiyar kasar Sin, kana jagoran tawagar kasar Sin da za su halarci taron kiwon lafiya na duniya (WHA) wanda za'a bude a Geneva a ranar Litinin. Ya bayyana a taron manema labarai cewa, Sin ta damu matuka game da halin da ake ciki na barkewar annobar cutar Ebola a DRC.
Alkaluma na baya bayan nan da mahukuntan DRC suka fitar ya nuna cewa, ya zuwa ranar Asabar adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar sun karu daga 17 zuwa 21.
Ma ya ce, a shekarar 2014 a lokacin da cutar Ebola ta barke a yammacin Afrika, gwamnatin kasar Sin da al'ummar Sin sun kai daukin gaggawa, Sin ta aike da kwararru da masana kiwon lafiya zuwa kasashen yammacin Afrika don bada taimako wajen shawo kan annobar cutar Ebola.
Ya kara da cewa, kasar Sin tana bibiyar yadda cutar Ebola ta barke a halin yanzu a DRC, ya ce idan an bukaci taimako, gwamnatin Sin da al'ummar Sinawa za su tura kwararru domin bada taimako. (Ahmad Fagam)