Ma Xiaowei, shugaban kwamitin lafiyar kasar Sin, kana jagoran tawagar kasar Sin mahalarta taron kiwon lafiya na duniya karo na 71 (WHA) wanda za'a bude a Geneva a ranar Litinin.
Ya bayyana a lokacin taron manema labarai a jiya Lahadi cewa, kasar Sin tana bada muhimmanci matuka wajen ceto lafiyar al'ummar kasarta, da inganta jin dadin rayuwar al'ummarta, kana kasar Sin tana taka rawa wajen tafiyar da harkokin kiwon lafiya na kasa da kasa.
A matsayinta na babbar kasa mai tasowa a duniya, kasar Sin ta samu nasarori masu tarin yawa a fagen tafiyar da harkokin kiwon lafiya kuma a shirye take ta yi musayar kwarewar da ta samu da sauran kasashen duniya, in ji mista Ma.
Ya ce a ayyukan da take yi tare da cibiyoyin bincike a Afrika, kasar Sin ta kaddamar da wasu ayyuka domin Afrika ta koya don amfanin al'umomin kasashen a bangaren rigakafi da magance cutar zazzabin malaria da dangoginsa, ya kara da cewa, kasar Sin ita ce ta farko a duniya wajen kaddamar da shirin kai daukin gaggawa. (Ahmad Fagam)