in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: A daina nunawa Zabiya bambanci
2018-06-14 10:44:03 cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira a da kawo karshen banbancin da ake nunawa Zabiya. Guterres ya yi wannan kiran ne a sakon da ya aike albarkacin ranar fadakar da jama'a ta duniya game da Zabiya.

Ya ce, da dama daga cikin wannan rukuni na mutane, wanda suka hada da yara da mata, na fuskantar hadari, da wariya a wasu lokutan ma har da cin zarafi da tashin hankali.

Jami'in na MDD ya ce, ko wane bil-Adama zai ci gajiyar ajandar samar da ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030, kuma wannan rana wata dama ce da za a nuna goyon baya da mutanen dake fama da wannan lalura, ta yadda za a hada kai don ganin su ma Zabiya sun rayu kamar kowa ba tare da nuna musu wata tsangwama ko wariya da fargaba ba. Har ma su more 'yancin rayuwa da ko wane bil-Adama ke samu.

Zabiya dai wata lalura ce dake shafar kwayoyin halitta, ba tare da la'akari da yare ko kabila ko jinsi ba a duniya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China