Cikin wata sanarwa da mataimakin kakakinsa Farhan Haq ya fitar, Mr. Guterres ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, tare da fatan samun sauki cikin sauri ga wadanda suka jikkata. Ya ce MDD na da yakini game da ikon kasar Somaliya, na ci gaba da fafutukar kawo karshen tashe tashen hankula, da wanzar da zaman lafiya, tare da samar da ci gaba mai dorewa.
Daga nan sai ya nanata kudurin majalissar, na ci gaba da marawa al'ummar Somalia da gwamnatin su baya, bisa wannan muhimmin kuduri.
A kalla mutane 15 ne suka rasu, yayin fashewar wasu bama bamai uku a birnin na Mogadishu. An ce bam din farko ya tashi ne a wani Otel, sai kuma wasu karin bama baman biyu, da suka biyo baya a wani wuri maras nisa daga na farkon.
Tuni dai kungiyar Al-Shabaab ta ayyana daukar alhakin kaddamar da hare haren. (Saminu Hassan)