Shugaba Rouhani, ya kuma shawarci kasar Turkiyya da ya ci gaba da gudanar da sahihin bincike, domin gano gaskiyar abun da ya auku.
Jamal Khashoggi, yana aiki ne da jaridar Washington Post, kuma mai fashin baki ne da ya jima yana sukar yarima mai jiran gado na kasar ta Saudiyya. An kuma hallaka shi ne a ranar 2 ga watan Oktobar nan, a karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Istanbul na Turkiyya.